Ingia
Ingia
Ingia
Chagua Lugha
026

Ash-Shuaraa 26:89 الا من اتى الله بقلب سليم ٨٩

26:89
إِلَّا
مَنۡ
أَتَى
ٱللَّهَ
بِقَلۡبٖ
سَلِيمٖ
٨٩
"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
Endelea Kusoma

Soma Tafsir

Ibn Kathir (Abridged)

The Prayer of Ibrahim for Himself and for His Father

Here Ibrahim, upon him be peace, asks his Lord to give him Hukm. Ibn `Abbas said, "This is knowledge."

وَأَلْحِقْنِى بِالصَّـلِحِينَ

(and join me with the righteous.) means, `make me one of the righteous in this world and the Hereafter.' This is like

…

The Prayer of Ibrahim for Himself and for His Father

Here Ibrahim, upon him be peace, asks his Lord to give him Hukm. Ibn `Abbas said, "This is knowled

…
Zaidi Tafsir

Soma Maudhui Yanayohusiana

Sura 26, Ukurasa 371, Juzuu 19

69. Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm. 70. A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa?" 71. Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su." 72. Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira?" 73. "Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku?" 74. Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa." 75. Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa?" 76. "Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa?" 77. "To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu." 78. "Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni." 79. "Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni." 80. "Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni." 81. "Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni." 82. "Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako." 83. "Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai." 84. "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe." 85. "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima." 86. "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu." 87. "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su." 88. "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi." 89. "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki." 90. Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa. 91. Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku. 92. Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?" 93. "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?" 94. Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun. 95. Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya. 96. Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, 97. "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna." 98. "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. 99. "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi." 100. "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta." 101. "Kuma bã mu da abõki, masõyi." 102. "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!" 103. Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba. 104. Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

- Hausa Translation(Abubakar Gumi)

Maelezo na Tafakari

Hakuna tafakari zilizokaguliwa kwa aya hii

Notes placeholders

Endelea Kuungana na Qur'ani ❤️

Vikumbusho vifupi vyenye maana vinavyoweka upya maisha yako, kukusaidia kutafakari na kuendelea kushikamana na Qur'ani.

Soma, Sikiliza, Tafuta, na Tafakari Qur'ani

Quran.com ni jukwaa linaloaminika na linalotumiwa na mamilioni duniani kote kusoma, kutafuta, kusikiliza na kutafakari kuhusu Qur'ani katika lugha tofauti. Inatoa huduma za tarjuma, tafsiri, vikariri, tarjuma ya neno kwa neno, na zana za ufahamu wa kina, kuifanya Qur'ani ipatikane na kila mtu.

Kama mbinu ya Sadaqah Jariyah, Quran.com imejitolea kusaidia watu kuunganishwa kwa kina na Qur'ani. Ikiungwa mkono na Quran.Foundation , shirika lisilo la faida la 501(c)(3), Quran.com inaendelea kukua kama rasilimali ya bila malipo na yenye thamani kwa wote, Alhamdulillah.

Chunguza
Nyumbani
Redio ya Qur'ani
Wasomaji
Kutuhusu
Watengenezaji
Sasisho za Bidhaa
Maoni
Msaada
Changia
Miradi Yetu
Quran.com
Quran For Android
Quran iOS
QuranReflect.com
Quran.AI
Sunnah.com
Nuqayah.com
Legacy.Quran.com
Corpus.Quran.com
Miradi isiyo ya faida inayomilikiwa, kusimamiwa, au kufadhiliwa na Quran.Foundation
Viungo Maarufu
Dua kutoka Quran
Aya ya Quran ya Siku
Ayatul Kursi
Yaseen
Al Mulk
Ar-Rahman
Al Waqi'ah
Al Kahf
Al Muzzammil
Ramani ya tovutiFaraghaSheria na Masharti
© 2026 Quran.com. Haki Zote Zimehifadhiwa
Changia