Kuma karantã musu1 lãbãrin ɗiya biyu2 na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."