Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga Manzon Sa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya1 (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.