"Waɗanda suke sunã bin Manzo1, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara.