Kanã iya jinkirtar da1 wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri.